Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har ila yau ta fadi cewa muna nuna cikakken goyon bayan mu ga kasar Tajikistan game da kokarinta na Yaki da ta’adanci, kuma iran tana kimanta aiki tare da take yi tsakaninta da kasar Tajikistan a bangarori dabn -daban da suka shafi tsaro dake da muhimmanci sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar Tajikistan
Tace” baya ga goyon bayan da iran ke bawa Tajikistan game da kokarin da take yi na yaki da ta’adanci, har ila yau ta bayyana shirinta na kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu wajen yin aiki tare na ganin an murkushe ta’adanci , haka zalika a shirye muke mu yi aiki da wasu kasashen ma a yankin wajen ganin haka ta cimma ruwa.
342/